Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Fadar White House ta tabbatar da harin da aka kai, An kuma ji karar harbe-harbe lokacin da rokokin ke sauka.
Harin rokokin na zuwa ne bayan wani harin da Amurka ta kai ranar Lahadi a Kabul, wanda ya yi sanadiyyar rayukan wasu fararen hula.
Shaidu ma sun ce mutane shida suka mutu a harin na jiya da Amurka ta yi amfani da jirgi marar matuki, ciki har da yara hudu, yayin da karin mutane da yawa suka kuma jikkata.
Amurka ta ce ta dakile harin kunar bakin wake, wanda aka yi nufin kai wa da mota a filin jirgin saman kasa da kasa na Kabul.
342/